1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kara wa´adin dokar Patriotic Act a Amirka da wata guda

December 23, 2005
https://p.dw.com/p/BvFN

A wani abin da ke zama koma baya ga shugaban Amirka GWB, dukkan majalisun dokokin kasar sun kara wa´adin dokar yaki da ta´addanci da aka sani da Patriotic Act da wata guda kacal. Majalisun dokokin sun ce hakan zai ba su damar yin nazari akan dokokin da suka shafi walwalar jama´a. Da farko shugaba Bush ya nema da aka kara wa´adin dokar na dindindin bayan dokar ta kare aiki a ranar 31 ga wannan wata na desamba. A cikin shekara ta 2002 aka kafa dokar yaki da ta´adanci bayan hare haren ta´addancin da aka kaiwa biranen New York da Washington. Fadar White House ta ce zata ci-gaba da matsa kaimi har sai ta samu amincewar dindindin ga dokar, duk da wannan koma baya da aka samu akan dokar wadda ake kace-nace akan ta. Shugaba Bush na shan suka bayan da ya bayyana a fili cewar shi ya ba da umarnin yiwa ´yan kasar leken asiri cikin harkokinsu na yau da kullum ba tare da izinin kotu ba.