An karya yarjejeniyar tsagaita wuta ta Yaman
December 15, 2015Talla
Wakilai na gwamnatin Yaman da na yan tawaye na ci gaba da tattaunawa da zumar samar da sulhu a ƙasar Suizeland a ƙarƙashin jagorancin Majalisar Ɗinkin Duniya.Sai dai rahotannin da ke zuwa mana daga Yaman na cewar 'yan tawayen Houthis sun kashe farar hula guda bakwai a cikin wasu ruwan bama-bamai da suka yi a yau duk kuwa da yarjejeniyar tsagaita wutar da aka saka hannu a kanta.
Tun a cikin watan Maris da ya wuce ake gwabza kazamin fada tsakanin dakarun gwamnati masu samun goyon bayan Saudiyya;da kuma mayaƙan 'yan tawaye Houthis 'yan Shi'a masu samu tallafi ƙasar Iran.