1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kashe ministan masanaantu na Lebanon

November 21, 2006
https://p.dw.com/p/Buat

A yau da rana ne wasu yan bindiga suka harbe ministan masaaantu na kasar Lebanon Pierre Gemayel wanda baya goyon bayan Syria a yayinda tawagarsa ke ratsawa kan wani titi a birnin Beirut.

Gamayel dan shekaru 34 a duniya ya goyi bayan wata kuria da majalisar zartarwa tayi na amincewa da shawarar Majalisar Dinkin Duniya cewa,kotun kasa da kasa ta saurari shariar wadanda suka kashe tsohon firaminista Rafik hariri wanda aka kashe a 2005.

Jakadan kasar Amurka a majalisar John Bolton ya jaddada cewa kashe ministan a yau ya sanya dole ne a gaggauta gurfanar da wadanda suka kashe Hariri yana mai nuna goyon bayansa ga gwamnatin Fouad Siniora

Kasashen duniya da dama dai sunyi Allah wadai da wannan kisa.

Saad Hariri dan tsohon Firaminista Hariri da aka kashe a 2005 ya zargi Syria da hannu cikin wannan kisa,kodayake Syria ta karyata tana mai Allah wadai da kisan Gemayel.