1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kashe mutane 13 a harin Porthacourt,Nigeria

January 1, 2008
https://p.dw.com/p/Civ2

Tsagerun Niger Delta ɗauke da makamai sun kai hare hare yau a wasu cibiyoyi a birnin Porthacourt,mai albarkatun mai,inda suka kashe mutane 13.Rahotannin jamian tsaro daga jihar dai na nuni dacewar,wayannan yan ta kifen sun kai wannan hari ne a ofisoshin yansanda guda biyu ,da kuma wani ginin Hotel.Kakakin Soji Lt Col Sagir Musa ya fadawa manema labaru cewar wadabda suka rasa rayukasnsu a harin na safiyar yau,sun hadar da jamian yansan 4,da fararen hula 3,kana da 6 daga cikin masu kai harin.Lt Col Musa dai ya dora alhakin wannan harin a wuyan wata kungiyar tsageru dake karkashin jagorancin Ateke Tom.Kakakin kungiyar 'Yan daban Richard Akinaka,ya faɗawa kamfanin dillancin labaru na Associate press ta wayar talho,sune suka kai harin .