1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kashe sojoji uku a côte d'ivoire

Mouhamadou Awal Balarabe
July 15, 2017

Hukumomin tsaro sun tabbatar da mutuwar sojoji uku bayan barkewar harbe harbe a barikin sojojin da ke arewacin Côte d'Ivoire a daren jiya Juma'a.

https://p.dw.com/p/2gaz8
Elfenbeinküste Soldatenmeuterei
Hoto: Getty Images/AFP/I. Sanogo

Mazauna Abidjan da Korogho da ke arewacin côte d'Ivoire sun ji karar harbe-haren bindigogi a barikokin sojojin wadannan birane biyu. Sai dai ya zuwa yanzu ba a san musabbabin boren nasu ba. Wani mazaunin Abidan ya bayyana wa kanfanin dillancin labaran AFP cewar tun da misalin karfi daya da rabi na dare ne suka fara jin harbe-harbe a cikin sansanin sojojin ONUCI ta Majalisar Dinkin Duniya da ke Abidjan.

A Korogho ma dai kuratan sojoji ne suka yi harbe-harbe a sama ba tare da an san ko me dalili ba. Sai dai kuma kura ta lafa a wannan Asabar a cewar mazauna biranen biyu da abin ya shafa.

A watan Janairi da Mayun da suka gabata ma dai, sojojin da ke boren sun kwace makaman da aka ajiye a wasu ofisoshin 'yan sanda a Bouake, birni na biyu mafi girma, sannan suka ja daga a kofar shiga birnin saboda rashin biyansu hakkinsu. Amma daga bisani gwamnatin ta ba wa kowanne daga cikinsu miliyan 12 na CFA a matsayin alawus da suka bukata.

Sai dai wasu tsofaffin 'yan tawaye da ba a shigar cikin rundunar sojojin Côote d' Ivoire ba  sun nemi alawus ba tare da hakarsu ta cimma ruwa ba.