1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kashe sojojin Amirka guda biyu a yammacin Iraqi.

March 15, 2006
https://p.dw.com/p/Bv52

Hukumar rundunar sojin Amirka a Iraqi, ta tabbatad da rahotannin da ke nuna cewa, sojojinta guda biyu ne sukka sheƙa lahira, a wani ɗauki ba daɗin da wani rukunin dakarun Amirkan suka yi da `yan tawaye a jihar Al Anbar da ke yammacin ƙasar.

Kawo yanzu dai, yawan sojojin Amirka da suka rasa rayukansu a Iraqin, tun da aka afka wa ƙasar shekaru uku da suka wuce, ya kai dubu 2 da dari 3 da 9, bisa wasu alƙasluman da ma’aikatar tsaron Amirkan wato Pentagon ta buga.