1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon hari a kasar Mali kan sojoji

Gazali Abdou TasawaMay 19, 2016

Sojojin kasar Chadi biyar da ke cikin rundunar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a Mali MUNISMA sun halaka a cikin wani harin ta'addanci da aka kai kan ayarin motocinsu.

https://p.dw.com/p/1Iqeq
Symbolbild Rebellen Mali Timbuktu Weltkulturerbe zerstört
Hoto: dapd

An dai kai wa sojojin na MUNISMA ne a yankin Kidal da ke Arewacin kasar ta Mali, yankin da ke fama da rashin tabbas na tsaro. Rundunar ta MUNISMA wacce ta tabbatar da afkuwar lamarin cikin wata sanarwa da ta fitar, ta ce an kai harin ne a Laraba 18 ga wannan wata na Mayu da muke ciki da misalin karfe biyar na yamma agogon GMT a Arewacin garin Aguelhok, a dai-dai lokacin da ayarin motocin sojojin rundunar ke rakiyar wasu motoci masu dauke da kaya. Daya daga cikin motocin da ke ayarin na MUNISMA ce ta taka nakiya, kafin daga bisani maharan suka bude wuta nan take kan ayarin motocin. Rundunar ta MUNISMA dai ta tabbatar da kame wasu mutane uku da ake zargi da hannu a cikin wannan hari wanda kuma ta ce tuni ta mika su ga hannun mahukuntan kasar ta Mali.