1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kashe wani fitaccen dan jarida a Pakistan

Zainab Mohammed AbubakarMay 8, 2016

A birnin Karachin kasar Pakistan wasu 'yan bindiga sun kashe Khurram Zaki, dan jarida kuma mai fafutukar kare 'yanci ta shafukan sada zumunta na yanar gizo.

https://p.dw.com/p/1Ik5t
Pakistan Karatschi Beerdigung Khurram Zaki
Hoto: Reuters/A. Soomro

Mai shekaru 40 da haihuwa Khurram Zaki, yana zaune a wani wurin cin abinci da ke gefen titi tare da abokinsa, lokacin da wasu 'yan bindiga guda hudu akan babubura biyu suka buda masa wuta, acewar jami'in dan sanda Arab Mehar.

Kafin mutuwar tasa Khurram, ya yi suna wajen nuna adawa da kungiyoyin tarzoma , da suka hadar da Taliban na Pakistan.

Kafin rasuwarsa ya jagoranci gangamin adawa da Maulana Abdul Aziz, wanda ya zarga da yin wa'azin janyo kiyayya tsakanin al'umma a wani masallaci da ake kira Red Mosque a birnin Islamabad.

Mayakan taliban na Pakistan dai na yawaita kai hari a Karachi, birni mafi girma a Pakistan, wanda ke dauke kabilu daban daban.