1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kashe ´yan tawayen Taliban su 30 a kudancin Afghanistan

June 10, 2006
https://p.dw.com/p/Buuc
Rundunar sojin Amirka a Afghanistan ta ce dakarun kasar Kanada da takwarorinsu na Afghanistan sun halaka mayakan Taliban fiye da 30 a cikin makon da ya gabata. A cikin wata sanarwa da dakarun dake karkashin jagorancin Amirka a Afghanistan ta bayar ta nunar da cewa an kaiwa ´yan tawayen hari ne a lardin Zabul dake kudancin kasar. Sanarwar ta ci gaba da cewa babu sojan kawance ko daya da ya ratsa ransa sakamakon gumurzun da aka yi. A wani hare-haren da aka kai jiya juma´a an halaka akalla mutane 13 ciki har da ´yan Afghanistan su 2 dukkan su ma´aikatan wata kungiyar ba da agaji. ´Yan sanda sun zargi mayakan Taliban da hannu a wadannan hare haren.