1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kawo ƙarshen fashin wani jirgin saman Turkiya cikin lumana

August 18, 2007
https://p.dw.com/p/BuDk

Mutanen nan biyu da suka yi kokarin fashin wani jirgin saman fasinja na kasar Turkiya sun yi saranda ga hukumomi bayan da jirgin ya sauka a kudancin Turkiya. Mutanen biyu wadanda suka hada da Bafalasdine dake amfani da fasfo din kasar Syria da kuma wani dan Turkiya sun yi ikirarin cewa sun ´yan kungiyar al-Qaida ne bayan sun yi fashin jirgin jim kadan da tashin sa daga arewacin tsibirin Cyprus. Sun yi ikirarin cewa suna dauke da bam inda suka bukaci da ajuya akalar jirgin dake dauke da fasinjoji 140 zuwa Iran ko Syria, amma jirgin ya sauka a kudancin Turkiya bayan da matukinsa ya ce dole ya sake shan mai. Matukan jirgin da sauran fasinjoji sun tsere daga cikin jim kadan bayan saukarsa. Ma´aikatar harkokin wajen Iran ta yi tir da fashin tana mai cewa da ta yi biris da bukatun ´yan fashin na neman sauka a Iran.