1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kawo ƙarshen taron shugabannin kabilu na Pakistan da Afghanistan

August 12, 2007
https://p.dw.com/p/BuEA
Tare da yin kira na samar da zaman lafiya da bawa juna hadin kai, an kammala taron majalisar daruruwan shugabannin kabilu na kasashen Afghanistan da Pakistan a birnin Kabul. Shugaban Pakistan Pervez Musharraf wanda ya halarci zaman karshe na taron wanda ake kira taron Jirga a babban birnin Afghanistan, ba kamar yadda aka saba ba ya fito fili ya amsa cewa Pakistan ma tana da nata laifin dangane da sake farfadowar kungiyar Taliban ta masu kishin Islama. Duk da hada karfi da karfe da ake yi don yakar Taliban, kungiyar ta sake kai hari kan wani sansanin sojin Amirka dake kudancin Afghanistan karo na 3 cikin kwanaki kalilan. Dakarun Amirka sun nunar da cewa nan ba da dadewa ba ´yan tawayen Taliban zasu yi kokarin farma sansanin na Anaconda dake lardin Urusgan.