1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kawo karshen fashin jirgin saman Turkiya

October 4, 2006
https://p.dw.com/p/BuhQ

Jirgin saman yana kann hanyarsa ce daga Albania zuwa birnin Istnabul lokacinda wani mutun ya baiwa matukin jirgin umurnin ya juya akalarsa zuwa Rom.

Sai dai maaikatan cikin jirgin sun yi sigina biyu dake nuna alamar anyi fashin jirgin,daga nan kuma jiragen yakin Italiya biyu suka tilasatawa jirgin sauka garin Brindisi dake kudancin kasar,inda dan fashin yayi saranda.

Yan sanda sunce subyi imain cewa mutumin shi kadai yake aiki amma suna bincike game da rahoton dake nuna cewa su biyu ne suka kaddamar da harin.

Jamian kasashen Turkiya dana Italiyan sunce mutumin tsohon soja ne da yayi bijire daga rundunar sojin Turkiya yana mia neman mafakar siyasa a kasar Italiya.

Hukumomin kasar sun karyata rahotannin farko dake cewa fashin jirgin wani martani ne game da ziyara da fafaroma Benedict na 16 yayi niyar kaiwa kasar Turkiya.