1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kawo karshen tarzoma data barke a gidan yarin Kabul

March 1, 2006
https://p.dw.com/p/Bv6J

Mahukunta a kasar Afghanistan sun samu sukunin shawo kann tarzomar data barke a cikin gidan yarin birnin Kabul.

Tarzomar da aka shafe kwanaki kusan hudu ba tare da shawo kann ta ba, ya zuwa yanzu bayanai sun nunar da cewa tayi asarar rayuka a kalla 6 da jikkata wasu 40.

A cewar mataimakin ministan shari´a na kasar tuni aka canzawa fursunonin da ake zargi nada hannu a cikin wannan tarzoma gurin zama.

Rahotanni dai sun tabbatar da cewa daga cikin fursunoni 1, 300 da ake zargi nada hannu a cikin wannan tarzoma guda dari 3 daga cikin su yan kungiyyar taliban ne da kuma Alqeeda.

Fursunonin dai na zargin gwamnati ne da ci gaba da tsare su ba tare da gurfanar dasu a gaban kuliya ba, kana a hannu daya kuma da nuna fushin su a game da dokar saka su sanya kaya na bai daya.