1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An koma kan teburin shawarwari tsakanin cocin Evangelika da kungiyoyin Musulmi a Jamus

Mohammed Nasiru AwalJune 7, 2007

Tun kimanin watanni shida da suka wuce shawarwari tsakanin sassan biyu suka cije.

https://p.dw.com/p/BvSr
Wolfgang Huber shugaban majalisar cocin Evangelika a Jamus
Wolfgang Huber shugaban majalisar cocin Evangelika a JamusHoto: AP

Jama´a masu sauraro barkanku da warhaka, barkanmu kuma da saduwa da ku a cikin wani sabon shirin an Taba Ka Lashe, shirin da ke duba batutuwan da suka shafi al´adu, addinai da zamantakewa a sassa daban daban na duniya.

Tun kimanin watanni 6 da suka wuce aka katse tattaunawar neman fahimtar juna tsakanin manyan shugabannin majami´ar Evangelika a Jamus da kuma manyan kungiyoyin musulmi dake wannan a kasa. An shiga wannan hali ne sakamakon buga wani karamin littafi da majami´ar Evanglika ta yi, mai taken bayanai daki-daki da kyakkyawar makwabtaka tsakanin kiristoci da musulmi a Jamus wanda ake yi ta kai ruwa rana kai. Al´umar musulmi a nan kasar sun fusata game da wasu kalamai game da addinin Islama da kuma musulmi kansu da ke kunshe cikin littafi. To amma duk da haka a tsakiyar makon jiya wakilan sassan biyu sun gana a matsallacin Yavuz-Sultan-Selim dake birnin Mannheim don ci-gaba da tattaunawar ta neman fahimtar juna duk da bambamce bambamcen dake akwai har yanzu a tsakanin su. To ko shin wannan ganawar ta yi armashi bayan an shafe watanni 6 ba tare da an tuntubi juna ba, muna dauke da karin bayani a cikin shirin na yau wanda ni MNA zan gabatar.

Musik..................Musik

Bekir Alboga wakilin kungiyar Turkawa musulmi dake kula da sha´anin addini a Jamus wato Ditib ya bayyana a takaice cewar taron na birnin Mannheim yana da muhimmanci musamman kasancewar har yanzu akwai sabanin ra´ayi tsakanin manyan shugabannin majami´ar Evangelika da wakilan kungiyoyin musulmi a Jamus.

1. O-Ton Alboga:

“Sakon da nake da shi ga kowa shi ne za´a ci-gaba da wannan tattaunawa, domin ta haka ne kawai za´a samu karfin guiwar musayar ra´ayoyi. Ina farin ciki da komawa kan teburin tattaunawar.”

Shi ma shugaban sashen da ya tsara kuma ya kula tare da buga dan karamin littafin na majami´ar Evangelika Jürgen Schmude ya ce ba bu zabi face a ci-gaba da tattaunawar tsakanin musulmi da kirista don samun fahimtar juna.

2. O-Ton Schmude:

“Har yanzu dai akwai sabani. To amma shirin da aka nuna game da yin aiki tare don samun masalaha, zai tabbatar nan ba da dadewa ba cewa taron namu yana yin armashi kuma zamu ci-gaba da haka.”

Sannu a hankali ne dai aka fara samun wannan sabani. Littafin farko da majami´ar ta Evangelika ta buga kan zamantakewa tsakanin kiristoci da musulmai a cikin shekara ta 2000, ya samu karbuwa musamman daga bangaren musulmi a wannan kasa. Dukkan sassan biyu ne kuwa suka tsara abubuwan da littafin ya kunsa. A ciki an yi bayani game da dangantaka tsakanin addinan guda biyu tare da yin kira da a kyautata bangarorin da addinan suka dace akai sai kara yin bayani a wurare da aka samu sabani. To amma sai a cikin litafin na biyu aka mayar da hankali wajen mayaar da addinin Islama saniyar ware. Mista Schmude yace dagangan aka tsara wadannan kalmomi masu tsauri domin manufa ita ce a tabka wata zazzafar muhawwara da musulmin.

3. O-Ton Schmude:

“Yanzu an shiga wani lokaci na yin bayanai dalla-dalla. Da ma manufar mu kenan domin mun san irin alfanu da kuma fa´idar dake tattare da haka. A sane mu ka yanke wannan shawara domin mu iya gabatar da tambayoyi da kuma nuna matsayin mu. Saboda haka yanzu muna jira ne a yi mana bayani a game da wadannan tambayoyin ko sun yi daidai ko kuma ana bukatar gyara.”

Ga ra´yin wakilan kungiyoyin musulmi dai littafin na kunshe da wasu sassa wadanda ko kadan ba su dace da tattaunawar samun fahimtar juna tsakanin mabiya addinai dabam-dabam ba. Alal misali suna zargin majami´yar Evangelika da yin amfani da littafin wajen yin kira ga kiristoci da su shawo kan musulmi su yi ridda, wato su saki musulunci suka kama addinin kirista. To amma rashin fahimta ne inji Bishop Wolfgang Huber shugaban majalisar cocin Evangelika a Jamus. Ya ce yin bayani game da addinin da mutum ya yi imani da shi wani bangare na yin tattaunawa ta gaskiya sannan sai ya kara da cewa.

4. O-Ton Huber:

“Idan ka duba a cikin dukkan dokokin majami´ar Evangelika a Jamus game da aikin mishan, zaka ga cewar muna girmama dukkan wadanda suka yi imani da addinin su. Saboda haka ba mu taba yin tunanin tilastama wani barin addini sa don ya shigo na mu ba.”

Duk da wadannan bayanai dai, wakilan kungiyoyin musulmi na ci-gaba da nuna rashin gamsuwarsu da littafin na cocin Evangelika. Suka ce a cikin littafin an yi ta maimaitawa tare da karfafa wasu kalamai na nuna wariya da addinin Islama. Hakan uwa ba abin karbuwa ba ne ga musulmi inji Bekir Alboga na kungiyar Ditib.

5. O-Ton Alboga:

“Abin bakin ciki ne yadda muka ga littafin ya kunshi dukkan bambamce bambamce da wariyar da ake nuna mana a kan titi da wuraren cin abinci da dai sauransu. Tsammani na zamu shiga tattaunawa ne da shugabanni. To amma wannan matsayin na su ba ruwansa da wata tattaunawa mai armashi, domin littafin ya karfafa nuna mana wariya.”

Shi ma Ayyub Axel Köhler shugaban majalisar tsakiya ta musulmi a Jamus kuma jagoran hadaddiyar majalisar musulmi wadda ta kunshi mayan kungiyoyin musulmi 4 ya ce ba zai yiwu a yi wata tattaunawa tsakani da Allah ba sakamakon wannan littaffi.

6. O-Ton Köhler:

“Na yi imani cewa yanzu majami´ar Evangelika ta gane cewar ba zata iya ci-gaba da tattaunawa da wannan matsayi na ta.”

To amma a nasa bangaren Bishop Huber ya kare matsayin cocin yana mai cewa an samu ci-gaba bisa manufa sakamakon wannan littafi. Yace tattaunawar ta birnin Mannheim tav fi sauran da aka yi a baya armashi, duk da sabanin da aka samu. Duk da haka a shirye majami´ar Evangelika ta ke ta canza matsayinta idan da akwai kwararan dalilan yin haka, inji Jürgen Schmude shugababn sashen da ya tsara littafin.

Tun bayan watan janerun shekara ta 2005 da watan maris na shekara 2006, taron na birnin Mannheim shi ne na 3 tsakanin shugabannin manyan addinan biyu. Trao na gaba wanda ake sa ran yin sa a wani lokaci cikin wannan shekara, majami´ar Evangelika a Jamus ce zata dauki nauyin gudanarwa a cikin wani cocin ta.