1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An koma Sharair Saddam

Hauwa Abubakar AjejeMay 15, 2006

Tsohon shugaban na Iraqi,ya kangare yaki amsa tuhuma da kotu tayi masa

https://p.dw.com/p/Bu07
Hoto: dpa-bildfunk

A karo na farko tun da aka fara shariar ta Saddam a watan oktoba,a yau kotu ta caje shi da laifin take hakkin dan adam,inda alakali Rauf Abdel Rahman ya karanto jerin zarge zarge da akeyiwa Saddam,wadanda suka hada da kashe yan shia 148 bayan wani yunkurin kashe shi da akayi a 1982 a garin Dujail.

Alkalin yace tsohon shugaban na Iraqi ne ya bada umurnin kashewa tare da azabtar da daruruwan mutanen kauyen,ciki har da mata da yara kanana,ya kuma aika da jirage da sukayi luguden wuta akan garin na Dujail dake arewacin birnin Bagadaza.

Saddam dai sai murmushi yakeyi alokacinda alkali yake karanta wadannan laifuka nasa,inda yace babu abinda zai girgiza shi,yace abinda ya dame ni kawai shine jamaar kasar Iraqi da ni kaina,nine shugaban kasar Iraqi,kamar yadda jamaa suka shaida.

Alkalin ya kuma kira jerin sunayen wasu 32 cikin mutum 148 da aka kashe a Dujail,wadanda yace yan kasa da shekaru 18 ne kuma bai cancanta a yanke musu hukuncin kisa ba karkashin dokar kasar dama dokar kasa da kasa.

Idan dai an kama su da wadannan laifuka,saddam dan shekaru 69 da mukarrabansa 7 wadanda dukkaninsu suka ki amsa laifukan da ake zargin su zasu fuskanci hukuncin kisa.

A kasar ta Iraqi kuma,yan bindiga sun kakkabo wani jirgi mai saukar angulu na Amurka,lokacinda ake musayar wuta a kudancin Bagadaza,inda sojin Amurka 2 suka rasa rayukansu.

Wannan abu kuwa ya abku ne a kusa da garin yusufiya dake da tazarar kilomita 15 daga kudancin Bagadaza,inda sojin sa kai suke ci gaba da kai hare hare tun lokacinda Amurka ta mamaye Iraqi.

Sojin na Amurka suma a nasu bangare suna ci gaba da kai farmaki akan sojin sa kai na yankin Yusufiya,inda suka baiyana cewa,cikin su har da Abu Musab al Zarqawi shugaban AlQaeda a Iraqi.

A farkon wannan wata ne kuma rundunar sojin Amurkan tace ta gano wasu takardu da kuma kaset na bidiyo mai dauke da hoton Al Zarqawi a garin na Yusufiya,haka kuma suna nan suna ci gaba da farautarsa.

Yanzu daya rage waadin kasa da mako guda ga firaminsta Nuri al-Maliki ya mika sunayen ministocinsa bisa tsarin Hadaka,da Amurka take ganin zai kawadda fadawar kasar cikin yakin basasa,har yanzu shugabannin adawa suna gwagwarmayar cimma matsaya akan batun nadin ministocin.