1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kori 'yan sanda 200 a Ruwanda

Abdul-raheem Hassan
February 6, 2017

Gwamnatin kasar Ruwanda ta kori jami'an 'yan sanda 200 daga aiki bisa zarginsu da laifin cin hanci. Wannan dai yunkuri ne na tsabtace kasar daga aiyukan bata kasa..

https://p.dw.com/p/2X4To
Paul Kagame
Hoto: picture-alliance/dpa/S. Kolli

Wannan mataki dai na zuwa ne bayan da kungiyar da ke yaki da cin hanci da rashawa a dunya Transparancy International ta ayyana kasar Ruwanda cikin kasashen Afirka da ke samun raguwar cin hanci da rashawa bayan kasashen Bostwana da Cape Verde.

Kakakin rundunar 'yan sandan kasar Theos Badege, ya tabbatar da cewa babu sani ba sabo a yunkurin su na kauda kasar daga aiyukan cin hanci da karbar rashawa. A shekarar da ta gabata ma dai fararen hula kusan 200 ne da jami'an 'yan sanda 80 aka cafke kan karbar na goro a kasar.

Wasu daga cikin 'yan kasar na sukar yunkurin Shugaba Paul Kagame da take hakkin bil'adama, amma duk da haka wasu na ganin gwamnatin na cimma nasarar dakile ayiyukan rashawa a fadin kasar.