1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kussa kawo ƙarshen taƙƙadamar shari´ar likitocin nan na ƙetare a Lybia

July 17, 2007
https://p.dw.com/p/BuG6

Bisa dukkan alamu nas-nas ɗin nan 5 yan ƙasar Bulgaria da dokata ɗaya na ƙasar Palestinu sun ƙetara rijiya da baya.

A ɗazunan ne Ƙungiyar iyayen yaran nan 426, da gwamnatin Libiya ta ce wannan likitoci sun ɗuga masu ƙwayoyin cutar Aids, su ka buƙaci kotu ta janye hukuncin kissan da ta yanke masu.

Kakakin iyalan yaran, Idriss Lagha, ya bayyana wa manema labarai cewar, sun ɗauki wannan mataki bayan cikka dukan sharuɗan da su ka gitta na biyan diyya.

A halin yanzu a cewar sa, dukkan iyalan yaran sun samu diyyar da su ka tambaya.

Baki ɗaya an biya diyyar Euro Milion ɗari 4, wadda a ka rabawa iyalan wannan yara.

Ƙungiyar iyayen yaran, ta miƙawa gidauniyar Ƙaddafi da ke shiga tsakani, wasiƙa a rubuce, wadda zata gabatarwa kotunan Lybia.

Idan kotunan su ka amince da buƙatar, a na kyauttata zaton nan da yan sa´o´imasu zuwa, kotun ta janye hukunci.

An kama wannan likitoci tun shekara ta 1999, saidai sun ci gaba da mussantta lefin da a ke tuhumar su da aikatawa.