1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An mayar da bakin haure fiye da dubu daya zuwa Libya

Mohammad Nasiru Awal ATB
August 7, 2017

Masu tsaron gabar teku sun mayar da bakin haure fiye da dubu daya zuwa Libya bayan an ceto su daga tekun Bahar Rum.

https://p.dw.com/p/2hqBP
Libyen Migration
Hoto: picture-alliance/dpa

A cikin kwanaki kalilan da suka wuce masu tsaron kan iyakokin ruwan kasar Libya sun ceto bakin haure fiye da dubu daya daga kwale-kwalen katako da na roba a cikin tekun Bahar Rum, inda suka mayar da su kasar ta Libya mai fama da yakin basasa.

Kungiyar kula da hijira ta kasa da kasa ta ce tun daga ranar Jumma'a da ta gabata an ceto mutane 1124 daga teku.

Kafafan yada labarun kasar Italiya sun ce wadanda aka ceton sun fito ne daga kasashen Maroko, Tunesiya, Aljeriya, Sudan da wasu daga kasashen Afirka na Kudu da Sahara da kuma kasar Siriya.

Kungiyoyin kare hakkin dan Adam dai sun sha yin gargadi game da mayar da bakin hauren kasar Libya, suna masu cewa sau tari bakin hauren na rayuwa cikin mawuyacin hali, ana kuma gana musu azaba.