1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An mikawa Annan rahoton binciken kisan gillan da aka yiwa Hariri

October 20, 2005
https://p.dw.com/p/BvOZ

Shugaban masu binciken kisan da aka yiwa tsohon FM Lebanon Rafik Hariri ya mikawa babban sakataren MDD Kofi Annan rahoton sa a yau alhamis. Alkali Detlev Mehlis bajamushe, wanda ya kware akan binciken ayyukan ´yan ta´adda ya ba Annan rahoton akan kisan da aka yiwa Hariri da wasu mutane 20 a birnin Beirut a cikin watan fabrairu da ya gabata. A wani lokaci nan gaba za´a gabatawar kwamitin sulhu na MDD wannan rahoto. Kisan dai ya sha tofin Allah tsine daga kasashen duniya da kuma jerin zanga-zanga a birnin Beirut abin da ya tilastawa Syria janye dakarunta daga Lebanon, bayan kusan shekaru 30 a wannan kasa. Kasashen duniya da dama sun zargi Syria da hannu a kisan na Hariri, amma gwamnati a birnin Damaskus ta musanta.