1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An nada sabon Firayim Minista na wucin gadi a Ivory Coast

Hauwa Abubakar AjejeDecember 5, 2005

An dai nada Charles Konan Banny,shugaban Babban bankin Afrika ta yamma a wannan matsayi

https://p.dw.com/p/Bu3h

Masu shiga tsakani na Afrika a rikicin na Ivory Coast suka yanke shawarar nada prime minister na wucin gadin a kasar,wanda ake ganin zai kawo karshen dambarwar siyasa a kasar.

Kasar ta Ivory coast mafi arzikin koko a duniya, ta rarrabu kashi biyu tun lokacinda yan tawaye suka kwace arewacin kasar, bayan da suka gagara habarar da shugaba Laurent Gabgbo shekaru uku da suka shige.

Shiryuka da dama na zaman lafiya da Majalisar Dinkin Duniya ta shirya a baya sun gagara cimma nasara a rikicin kasar ta yankin Afrika ta yamma.

Shugaba Obasanjo na Najeriya a wajen taron a birnin Abidjan yace,wannan nadi babbar nasara ce ga jamaar kasar Ivory Coast.

Yace babu wanda zai ce yayi nasara ko ya fadi a tsakanin gwamnati da yan tawaye.

Sabon shugaban wucin gadin an dora masa alhakin kwance damarar yakin yan tawaye da kuma yin gyare gyare da suka kamata kafin zaben shugaban kasa a karshen watan oktoba mai zuwa.

Dole ne bangarori dake yaki da juna a Ivory Coast su amince da nadin sabon Prime ministan na wucin gadi karkashin shirin wanzar da zaman lafiya na Kungiyar Taraiyar Afrika da komitin sulhu ya yarda da shi,sai dai da farko gwamnatin Gbagbo da jamiyun adawa da kuma yan tawaye sun ja da wannan batu na tsawon makonni kafin su yarda da shi.

Shugaban yan tawaye Guillaume Soro tun da farko ya so a bashi wannan matsayi na prime minister,domin suyi raba dai dai na ikon da shugaba Laurent gbagbo yake da shi,kodayake a yanzu kakakin Guillame yace kungiyarsu ta amince da nadin Banny a wannan matsayi.

Yace mun amince da wannan shawara,kuma muna fata prime ministan zai samu damar sauke nauyi da aka dora masa,ya kuma cika alkawari yayi aiki kamar yadda ake bukata.

Shima shugaban gamaiyar jamiyun adawa,Alphonse Djedje Mady ya fadawa kanfanin dillancin labarai na Reuters cewa sunyi maraba da wannan shawara.

Yace sunyi farin ciki game da wannan nadi kuma suna fata Banny zai samu nasarar gudanar da aiyukan da aka dora masa saboda jamaar Ivory Coast.

Banny shine shugaban babban bankin kasashen Afrika ta yamma,wadda yanzu haka kasashe takwas na yankin suke anfani da takardar kudinsa na CFA franc.

Karakashin tsarin mulkin kasar ta Ivory Coast wadda Faransa tayiwa mulkin mallaka dai,prime minister ba shi da iko mai yawa kamar na shugaban kasa,sai dai a wannan karo Majalisar Dinkin Duniya ta baiwa Banny Karin iko karkashin wata dokarta da ta sanya hannu akai a watan oktoba.

Wannan doka dai ta baiwa Gabgbo damar kasancewa bisa karagar mulki na tsawon shekara guda bayan waadin mulkinsa ya kare a ranar 30 ga watan oktoba bayan dakatar da zabe da aka shirya zaa gudanar a wancan ranar.

Tun da farko shugaban kasar Afrika ta kudu Thabo Mbeki,ya baiyana cewa,kin amincewa da nada sabon prime ministan na wucin gadi da zai kawo cikas ga jadawalin shirya zabe na kasar.