1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An nemi taimakon kasashen duniya kan matsalolin hijira

Suleiman BabayoSeptember 8, 2015

Ana ci gaba da mahawara kan shawo kan matsalolin bakin haure da 'yan gudun hijira a duniya.

https://p.dw.com/p/1GTCu
Griechenland Ausschreitungen zwischen Flüchtlingen und Polizei auf Lesbos
Hoto: Getty Images/AFP/A. Tzortzinis

Wani babban jami'in Majalisar Dinkin Duniya da ke kula da hijira ya ce matsalolin bakin haure da 'yan gudun hijira da ake samu abu ne da ya shafi duniya baki daya, kuma ya dace kowace kasa ta ba da taimakon da ya dace.

Peter Sutherland ya shaida wa manema labarai a birnin Geneva na kasar Switzerland cewar matsalolin da ake samu na duniya da ke neman warware daga kasashen duniya baki daya. Tuni kasashen Turai suka yi nisa da mahawara bisa matsalolin bakin haure.

Firaminista David Cameron na Birtaniya ya ce kasar za ta dauki 'yan gudun hijira 20,000, yayin da Faransa ta ce za ta dauki kimanin 24,000. Bernard Cazeneuve ministan harkokin cikin gida na kasar ta Faransa ya soki matakin wasu magadan gari a kasar wadanda suka ce za su amince da 'yan gudun hijira Kiristoci ne kawai. Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bukaci kasashen na Turai su yi amfani tsari bai daya na rarraba masu neman mafaka tsakanin kasashen nahiyar.