1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An nuna bukatar farfado da shirin samar da zaman lafiyar GTT

January 27, 2007
https://p.dw.com/p/BuT5

Jamus da Jordan sun kuduri aniyar karfafa kokarin da suke yi na ciyar da shirin samar da zaman lafiya a yankin GTT gaba. Bayan tattaunawar da suka yi da sarkin Jordan Abdullah na biyu a birnin Berlin, SGJ Angela Merkel ta ce yanzu akwai damar hada dukkan kokarin da kasashen duniya ke yi don samun mafita a rikicin na yankin GTT. Jordan ta nuna goyon bayan ta ga shirin nan na bangarorin nan 6 dake yin sulhu na GTT da suka hada da KTT, MDD, Amirka da kuma Rasha. SG ta Jamus ta karfafa kiran da ake yi da nufin samun wata maslaha ta kasashe biyu makwabtan juna a rikicin da ake yi tsakanin Isra´ila da Falasdinawa. A lokacin daya kuma Merkel ta ce dole ne a marawa masu fafatukar kafa mulkin demukiradiya a Libanon baya.