1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An rantsad da Kaczynski a mukamin sabon Firimiyan Poland

July 14, 2006
https://p.dw.com/p/Buqc
Shugaban Poland Lech Kaczynski ya rantsad da dan´uwan tagwaitakarsa Jaroslaw Kaczynski a mukamin sabon FM kasar. Rahotanni sun nunar da cewa bisa ga dukkan alamu a ranar laraba mai zuwa sabon FM zai fuskanci kuri´ar amincewa da shi a majalisar dokokin kasar ta Poland. A bara Jaroslaw Kacynski rikakken mai ra´ayin kishin kasa, ya ki karbar mukamin FM kasar ta Poland saboda ba ya son ya kawo wa dan´uwansa cikas a zaben shugaban kasar da aka gudanar. Jaroslaw dai shi ne shugaban jam´iyar ´yan kishin kasa wadda ta fi yawan wakilai a cikin gwamnatin hadin guiwa.