1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An rantsar da sabon firaministan kasar Ostareliya

Suleiman BabayoSeptember 15, 2015

Kasar Ostareliya ta samu sabon firaminista bayan sauyi da aka samu a shugabancin jam'iyya mai mulki wadda take da ra'ayin mazan jiya.

https://p.dw.com/p/1GWsr
Australien Malcolm Turnbull wird neuer Premierminister
Hoto: Getty Images/L. Coch

A wannan Talata an rantsar da Malcolm Turnbull hamshakin mai-arziki kana tsohon ma'aikacin banki a matsayin sabon firaministan kasar Ostareliya, wanda ya yi alkawarin samar da aiki da bunkasa tatttalin arzikin kasar. Turnbull ya maye gurbin Firaminista Tony Abbott bayan ya samu nasarar zaben shugabancin jam'iyya mai mulki, inda ya zama mutum na hudu da ya rike mukamun cikin shekaru biyu da suka gabata.

Sabon Firamnista Malcolm Turnbull na kasar ta Ostareliya dan shekaru 60 da haihuwa ya taba rike mukamun ministan sadarwa.