1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An rantsar da sabon shugaban ƙasar Pilipin

June 30, 2010

Mista Benigno Aquino shine shugaba na 15 da aka a samu a ƙasar Pilipin

https://p.dw.com/p/O6TU
sabon shugaban ƙasar Pilipin Benigno Noynoy AquinoHoto: AP

An rantsar da sabon shugaban ƙasar Pilipin Benigno Aquino,

Mista Aquino ɗan shekaru 50 da haifuwa ,wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar a ranar goma ga watan mayo, a gaban tsofon shugaban ƙasar Josephe Estrada, shine ɗaa tilo ga tsofon shugaban ƙasar na Pilipin Corazon Aquino, wanda ya yi gogormaya tabata da demokaraɗiya a ƙasar tun a shekara 1980.

Masu aiko da rahotanin sun ce du da ruwan saman da aka riƙa sheƙawa kamar da bakin ƙwarya mutame rabi miliyan ne suka hallarci shagulgulan bikin.

Mawallafi: Abdourahamane Hassane

Edita : Umar Aliyu