1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An rantsar da sabuwar Majalisar dokokin Turquia

August 4, 2007
https://p.dw.com/p/BuEk

Yau ne a ƙasar Turquia, ake rantsar da sabuwar Majalisar dokoki,wadda jam´iyar Praminista Tayib Recep Erdowan ke da gagaramin rinjaye a cikin ta.

Idan dai ba a manta ba, ranar 22 ga watan da ya gabata hukumar zaɓe, ta bayyana sakamakon zaɓen a hukunce, inda jama´iyar AKP ta sami kujeru 341 daga jimlar kujeru 550 da majalisar ta ƙunsa.

Sannan jam´iyar CHP ta zo sahu na 2, tare da yan majalisa 99.

A karon farko jam´iyar ƙurdawa ta samu kujeru 20,matsayin da ya zama wani abun tarihi a fagen siyasar Turquia.

Masharahanta a game da harakokin siyasar Turquia na tunanin cewar, Kurdawa sunshafui wannan majalisa, bisa dukkan alamu a dalili da matsin lambar da Turquia ke sha daga ƙetare.

Babban yaunin da ya rataya akan yan majalisar a halin yanzu shine, na zaɓen saban shugaban ƙasa.