1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An rantsar da Shimon Perez a matsayin saban shugaban ƙasar Isra´ila

July 15, 2007
https://p.dw.com/p/BuGG

Majalisar Dokokin Isra´ila,ta rantsar da Shimon Perez a matsayin saban shugaban ƙasa.

Peretz ɗan shekaru 83 a dunia, shine shugaban kasa na 9 a Israila, ya gaji shugaba Mosche Katzav ,wanda kotu ta tuhuma da lefin fyaɗe.

A cikin rantswuwar da yayi, ya alkawarta gudanar da ayuka ba tare da nuna banbanci , daidai da yadda kudin tsarin mulki ya tanada.

Kazalika ya alkawarta gudanar da aiki tuƙuru, domin kare yancin Isra´ila, da kuma haɓɓaka tattalin arzikin ta.

Saban shugaban ƙasar ya riƙe maƙamai ,daban -daban,wanda su ka haɗa da na Praminista har sau 2, da kuma ninistan harakokin waje, da na tsaro,da ministan kuɗi.

A lokacin da ya riƙe mukamin ministan tsaro Shimon Peretz ya ƙaddamar da tsarin samar da makamin nulkea ga ƙasar Isra´ila.