1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An rantsar da shugaba Kabila a birnin Kinshasa

Mohammad Nasiru AwalDecember 6, 2006

Dubun dubatan mutane suka hallara a gaban fadar shugaban kasa don shaidar da bukin na yau.

https://p.dw.com/p/BtxD
Shugaban Kongo Joseph Kabila
Shugaban Kongo Joseph KabilaHoto: AP

Bukin rantsad da Joseph Kabila ya zo ne a daidai lokacin da shirin janye sojojin kiyaye zaman lafiya na KTT ya kankama, inda ake sa ran kammala janyewar su daga wannan kasa dake yankin tsakiyar Afirka kafin karshen wannan shekara. Kungiyar EU ta ce zata ci-gaba da taimakawa Kongo ne da kudade, inda kungiyar ta ware Euro miliyan 400 a matsayin taimakon raya kasa ga Kongo nan da shekara ta 2013. Ko shakka babu shugaba Kabila na matukar bukatar wadannan kudade na taimako.

Tun yana da shekaru 29 Kabila ya dare kan kujerar shugabancin kasar ta JDK, bayan kisan gillar da aka yiwa mahaifinsa. Tun daga yau kuwa Kabila Junior ya zama shugaba kasar na farko da aka zaba ta hanyar demukiradiya a cikin shekaru 40.

Kabila ya lashe zagaye na biyu na zaben da kashi 58 cikin 100 akan mai kalubalantar sa Jean Pierre Bemba. Masharhanta na ganin wannan zaben a matsayin wani kyakkyawan mataki na samar da zaman lafiya ba a Kongo din ba kawai ba a´a har da ilahirin yankin baki daya.

“Al´umar Kongo na muradin samun zaman lafiya da ci-gaba. Saboda haka suke bukatar wata sahihiyar gwamnati wadda zata duba bukatunsu.”

A lokuta da dama Kabila yayi ta ganawa da madugan ´yan tawaye da wakilan kasashen Uganda da Rwanda da nufin samar da zaman lafiya mai dorewa a kasarsa. Domin har yanzu sojojin sa kai da ´yan takife na ci-gaba da aikata ta´asa musamman a gabashi da kuma arewacin kasar, duk kuwa da yarjejeniyar shekara ta 2002, wadda a hukumance ta kawo karshen yakin nan da ake yiwa lakabi da yakin duniya na daya a Afirka.

Yanzu dai an sa ido domin a ga kamun luden Kabila wanda shi ne shugaba mafi karancin shekaru a duniya. Dole ne Kabila ya samar da yanayi na bin doka da oda musamman a cikin rundunar sojin kasar, inda ake fama da rashin biyayya a tsakanin sojoji. Dole ne kuma ya dauki matakan kawo karshen wasoson da ake yiwa albarkatun kasa da Alah ya horewa Kongo.

“Da kudaden shigar da muke samu daga ma´adinai zamu iya sake gina kasar mu. Masu zuba jari na son riba, amma dole ne ita kuma kasa ta samu na ta rabo.”

To sai dai kafin al´umar kasar ta Kongo su kimanin miliyan 60 su ci gajiyar arzikin da Allah ya ba wa kasar, watakila sai bayan wasu shekaru masu yawa nan gaba.