1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An Rantsar da yayan majalisar dokokinn kasar Somalia a jiya

Mansour bala BelloAugust 23, 2004

bayan shekaru sama da goma sha ukku ana fafatawa a can kasar Somalia a tsakanin manyan kabilun kasar a jiya an fara daukar matakai na gyara domin tabbatar da kasancewar kasar ta sami alkibla.

https://p.dw.com/p/Bvh6
Hoto: dpa

Ministan harkokin karfafa huddar dangantaka a tsakanin kasashen dake yankin na kAsar Kenya John Koch yace wannan wata gagarumin nasara ce da aka samu a matakin karshe na tabbatar da doka da oda a kasar ta somaliya bayan cimma daidaito a tsakanin shugabannin lardunan kasar Baki daya .An dai gudanar da wannan rantsuwa ne a ofishin MDd a kasar Kenya inda mInistan ya gargade su da kasancewa jakadun wanzar da zaman lafiya maimakon yaki da juna wanda ya haifar da kisan alummar kasar a baya ..An dai dauki gabarar gudanar da wannan biki ne a Nairobi maimakon babban birnin kasar ta Somalia Mogadishu bisa matakan tsaro .Shugaban dake shiga tsakanin bangarorin da basa ga maciji da juna ya tabbatar da cewa a yanzu rana ta fito a tsakanin alummar kasar ta inda zaa zauna a inuwa daya domin warware rikicin dayaki yaki cinyewa a kasar musamman ta fannin tuntubar juna .Shugaban dai Betheul Kiplagat yace zaa cigaba da wannan mataki har sai an dawo da martabar kasar a cikin gida da kuma wajenta ..A daura da haka ne sakatare janar na MDd Kofi Annan ya aike da takardar yabo tare da murana bisa wannan gagarumar nasara tare da fatan cewa hakan zai dore .Yace an kwashe shekaru biyu ana wannan tattaunawa kuma a yanzu hakan ya cimma Ruwa .A daura da haka dai Kofi Anna ya jinjinawa Gwamnatin shugaba Mai kibaki bisa wannan namijin kokari baya ga kungiyar Igad da kuma yayan kasar ta Somaliya wadanda ke muradin wanzar da zaman lafiya a kasar ..A yanzu haka dai a kalla an zabi yayan majalisar dokokin sama da 275 a karon farko tun bayan kifar da gwamnatin Saad baaare a shekara ta 1991.To sai dai wata majiya na cewa wasu daga cikin yan kasar sun kauracewa wannan shirin bisa wasu matakai da suka dauka na cigaba da fafatawa da duk wanda ke neman wanzar da zaman lafiya a kasar .Bugu da kari Ministan Koch da kansa ya tabbatar da cewa har kawo yanzu akwai sauran rina a kaba a dangane da wainar siyasar kasar gta somaliya sai dai kuma namn bada jimawa ba zaa iya cimma manufa daya .Kamar dai yarda daya daga cikin wakilai na kungiyar gamaiyar Turai a kasar ta Kenya yace batun lardin Puntland ya kasance batun da zai haifar da sarkakkiya a dangane da wannan shiri bisa ballewar da yankin yayi a shekara ta 1998 to sai dai har kawo yanzu yyankin na ansa sunan kasar somaliya kuma tuni suka nada shugaban kasarsu mai suna Abdullahi Yusuf Ahmed dan kabilar Darod .Bugu da kari majiyar ta kara da cewa yankin arewa maso gabas ya bayyana ballewa daga kasar a shekara ta 1991 to sai dai hakan bai sami amincewar kasashen ketare ba kuma ilahirin yayan yankin sunki shiga wannan taro daya haifar da wadannan yayan majalisar dokokin kasar a halin yanzu .Yayan majalisar dokokin dai zasu kwashe shekaru biyar suna gudanar da aikin majalisa kafin a gudanar da sabon zabe .Ana cigaba da tattaunawa da manya manyan kabilun kasar su biyar domin kafa gwamnatin rikon kwarya tare da zabar shugaba a nan gaba .