1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An rufe taron NATO

Hauwa Abubakar AjejeNovember 29, 2006

Kungiyar tsaro ta NATO ta kammala taronta yau a Riga,tare da alkawarin ci gaba da aiyukanta na wanzar da zaman lafiya a kasar Afghanistan,tare da bada karin karfi ga dakarunta dake fafatawa da yan Taliban, da kuma batutuwa da suka shafi fadada kungiyar.

https://p.dw.com/p/BtxG
Jaap dev Hoop Scheffer
Jaap dev Hoop SchefferHoto: AP

Shugabannin kungiyar ta NATO a karshen taron nasu da aka gudanar a Riga babban birnin kasar Latvia sun sunyi gyara ga manufar kungiyar game da shigarda Serbia da Bosnia cikin kungiyar,inda suka mikawa kasashen biyu tayin matakin farko na shiga kungiyar,duk kuwa da batun wadanda suka aikata laifukan yaki a kasashen.

NATO ta gaiyaci Bosnia da Serbia tare da Montenegro shiga shirinta da tayiwa lakabi hadin kai don zaman lafiya,muddin dai sun bada cikakken goyon bayansu game da kame wadanda ake nema da laifukan yaki a lokacin yakin Bosnia.

A sanarwar hadin gwiwa da suka bayar shugabannin na NATO su 26 sun baiyana sadaukar da kansu ga ci gaba da goyon bayan hukumomin Afghanistan tare da hadin kan kasa da kasa.

sakatare janar na kungiyar Jaap de Hoop Scheffer yace akwai alamar samun nasara a kasar Afghanistan.

Firaministan Burtaniya kuma wanda dakarunsa tare dana kasashen Canada da Holland suke fuskantar tashe tashen hankula da hasasar sojojinsu yace shugabanin NATO sun amince cewa mutuncin kungiyar yana reto game da batun Afghanistan.

Shugaba Bush na Amurka kuwa cewa yayi zaa samu nasara ne idan kasashen kawance sun sadaukar da kawunansu,bayan komandojin kungiyar sun koka da yawan dakaru da mafi yawa na kasashen kungiyar suke kaiyadewa.

“samun nasarar NATO ya dogara ne kan komandojinta dake kasa wadanda dole ne su samu kayan aiki da ake bukata don gudanar da aikinsu.an kafa kungiyar ce bisa manufa dake baiyane.

Ya zuwa yanzu dai a cewarv kakakin Tony Blair kasashen Bulgaria da Spain da Macedonia dake neman shiga kungiyar sunyi tayin karin sojojinsu,haka kuma sakatare de Hoop Scheffer yace kasashen sunyi alkawarin taimakawa dakarunsu 26,000 dake kudancin Afghanistan.

“ba zai yiwuba ace dakarunmu dake kudancin kasar basu da kashi 20 cikin dari na abinda suke bukata”

Sai dai manyan kasashen kungiyar da dama kamar Faransa da Jamus da Italiya sunce,dakarunsu ba zasu bar inda suke ba sai

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel tace sun amince tsakaninsu cewa zasu taimakawa juna a yanayi

“muna taimakawa a duk inda aka shiga hali na bukata hakan yana bangare ne na aiyukanmu a kudancin kasar amma wurin daya kamata mu kasance bisa tsarin kungiyar shine arewacin kasar kuma banga yadda zamu kare arewacin kasar ba muddin mun koma kudancin kasar,amma duk da haka na dokanta akan tattaunawar siyasa don ganin an samu nasara akan aikinda ala sa a gaba a Afghanistan baki daya”

Shugabannin na NATO sun kuma mince da shawarar da Faransa ta bayar na kafa kungiyar tuntubar juna akan batun Afghanistan.

Kamar yadda ake zato kuma NATO ta tabbatar da aniyarta ta mikawa wasu kasashe dake neman shiga kungiyar gayyatar halartar babban taronta na gaba a 2008.

Kasashen kuwa sune,Croatia da Macedonia da Albania.