1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An rufe wani gidan radiyo a Uganda

Hauwa Abubakar AjejeAugust 12, 2005

An rufe gidan radiyon KFMa Uganda,biyowa bayan rahotanni game da musabbin hadarin da ya rutsa da John Garang

https://p.dw.com/p/BvaU
Yoweri Musaveni na Uganda
Yoweri Musaveni na UgandaHoto: AP

Jamian gwamnati dana gidan rediyon mai zaman kansa KFM,wanda shine kan gaba a babban birnin kasar,sun baiyana cewa gwamnati ta rufe gidan rediyon ne saboda abinda gwamanatin ta kira,kin bin dodokin yada labarai na kasar.

Minisatan yada labarai na Uganda ya fadawa kanfanin dillancin labarai na AFP cewa hukumar sa ido akan aiyukan yada labarai ta kasa ce ta ke aikinta.

Maaikatan gidan rediyon sun baiayana cewa hukumar ta aike da wasikar rufe gidan rediyon bayan zargi da tayi game da wani shiri da gidan rediyon ya yada ne a daren laraba.

Cikin wani shirin tattaunawa na saa guda da gidan rediyon yake yi a kowane mako, shirin na ranar laraba, ya tattauna barazanar da shugaba Museveni yayi ne na rufe wasu kanfanonin buga jaridu na kasar da suka buga rahotanni da basu da tushe game da hadarin jirgin sama da yayi sanadiyar mutuwar John Garang.

Gidan rediyon na KFM wani bangare ne na wani kanfanin buga jarida da Museveni yayiwa suka da laifin yada wani labarai game da mutuwar Garang da Musavenin ya ce barazana ce ga tsaron kasar.

Shugaban kanafanin jaridar Conrad Nkutu, ya baiyanawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa babu dalilin rufe wannan gidan rediyo kuma baya bisa kaida saboda haka zasu dauki mataki daya dace na ganin cewa gidan rediyon ya koma bakin aikinsa.

Haka itama kungiyar yan jarida ta Uganda UJA ta ce hukumar bata da iznin daukar wannan mataki.

Sakataren kungiyar,Haruna Kanaabi ya ce wannan mataki baya wani bangare na aiyukan hukumar ta kula da aiyukan yada labarai,wanda ya ce aikinta shine shiga tsakanin da sasanta duka wani rikici da ka iya tasowa tsakanin jamaa da kafofin yada labarai.

Shugaban kungiyar yan jaridun ya kuma yi kira ga yan kasar ta Uganda da kada su goyi bayan wannan mataki saboda a cewarsa yin hakan danne musu hakkinsu ne na fadin albarkacin bakinsu.

John Garang dai ya mutu ne a hadarin jirgi mai saukar angulu na shugaban kasar Uganda,hadarin da aka ce mai yiwuwa rashin kyan yanayi ne,ko duhu ko kuma kuskure na matukin jirgin,ya haddasa shi.

To sai dai rashin yarda da ainihin abinda ya haddasa hadarin, ya haddasa tashe tashen hankula a Sudan,wanda ya tilasata gwamantin Sudan din ta kafa wani komiti ciki harda kwarraru na kasa da kasa domin ya binciki musabbabin hadarin.

Kaffofin yada labarai na Uganda sun yi ta bada rahotanni iri daban daban game da wannan hadari,inda wasu suke cewa gawar John Garang da aka dauko daga wurin hadarin cike take da harsashen bindiga,wasu kuma sun ce yan zagon kasa ne daga Rwanda suka shirya wannan hadari.

Abin mamaki anan shine,shi kansa shugaba Museveni,shi ya fara fitowa fili yana fadin cewa bai tabbatar da cewa wannan hadari ne ba ,yana mai cewa mai yiwu ne akwai wani dalili daga waje.