1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An rushe majalisar dokokin Kuwaiti

May 21, 2006
https://p.dw.com/p/BuxN

Sarkin Kuwait Sheik Sabah Ahmed Sabah,ya rushe majalisar dokokin kasar a yau lahadi kuma yayi kira da gudanar da zabe cikin gaggawa,biyowa bayan rikici tsakanin gwamnatin kasar da mahukuntan kasar dangane da gyare gyare da suka shafi zabe a kasar.

Sheik Sabah ya bada umurnin gudanar da zaben majalisar dokoki a ranar 29 ga watan yuni maimakon shekara mai zuwa kamar yadda aka shirya tun farko .

Yan majalisar sun samu sabani tsakaninsu da yan majalisar zartaswa game da wata doka da zata rage yawan mazabu na kasar daga 25 zuwa 10,wanda yan majalisar suke nema a rage su zuwa 5,saboda rage abinda suka kira sayen kuriu.

A dai ranar laraba ne wasu yan majalisa 3 suka mika bukatar yiwa Firaminista tambayoyi game da wanna doka.

Wanna dai shine karo na 4 da masarautar ta Kuwait ta rushe majalisar dokokin kasar tun 1963.