1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An sa ranar zaben shugaban kasa a Masar

Ramatu Garba Baba
January 8, 2018

Shugaban hukumar zaben Masar Lasheen Ibrahim ya ce a ranar 26 zuwa 28 na watan Maris ne za a gudanar da zagayen farko na zaben shugaban kasa.

https://p.dw.com/p/2qXGu
Wahlen in Ägypten Stimmzettel
Hoto: Mohamed El Shahed/AFP/Getty Images

Lasheen Ibrahim ya ce za a je zagaye na biyu a ranakun 24 zuwa 26 na watan Afirilu idan har bukatar hakan ta taso. A yayin ganawarsa da manema labarai Ibrahim ya ce hukumar ta shirya don karbar takardun 'yan takara daga ranar 20 zuwa 29 na watan Janairu kafin daga bisani a wallafa sunayen 'yan takarar a manyan jaridun kasar a watan Febrairu.

Wannan na zuwa ne bayan da tsohon Firaminista Ahmed Shafiq ya sanar da cewa ba zai tsaya takara a zaben shugaban kasar ba duk da cewa a farko ana ganin Shafiq mai shekaru 76 wanda tsohon kwamanda na sojojin sama ne, kana tsohon firaminista karkashin tsohon Shugaba Hosni Murabak, a matsayin wanda zai zama kalubale ga Shugaba Abdel-Fatah al-Sissi wanda ake gani zai iya sake samun shugabancin kasar ta Masar cikin sauki a wannan zaben da ke tafe.