An sake bajamusa da aka sace a Iraqi(Osthoff)
December 19, 2005Talla
Maaikatar harkokin wajen Jamus ta tabbatar da sakin bajamushiya ta farko da aka taba sacewa a Iraqi Susanne Osthoff.
Ministan harkokin waje Frank-Walter Steinmeir, ya sanar cewa Osthoff tana cikin koshin lafiya a ofishin jakadancin Jamus dake birnin Bagadaza.
Osthoff da direbanta sun bace ne a ranar 24 ga watan nuwamba a arewacin Iraqi,inda daga bisani aka nuno su ta hanyar bidiyo idanunsu a rufe kuma kewaye da yan bindiga.
Ita dai Osthof musulma kuma mai jin harshen larabci,tayi aikin binciken kayan tarihi na karkashin kasa fiye da shekaru 10 a Iraqi.