1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An sake kai jerin hare haren bam a Iraƙi

January 22, 2007
https://p.dw.com/p/BuTe
An sake kai wasu tagwayen hare haren bam a Iraqi a wannan karo akan wata kasuwa dake garin Baquba na arewa maso gabashin kasar inda aka halaka akalla mutane 14. Da farko a yau wasu tagwayen hare hren bam da aka kai kan wata kasuwar sayar da gwanjo dake birnin Bagadaza, an halaka mutane akalla 75 yayin da samna da 150 suka jikata. Harin dai shi ne mafi muni tun bayan wasu tagwayen hare hare da aka kai a wajen harabar jami´ar Bagadaza wanda ya halaka mutane 70 kwanaki 6 da suka wuce. Wadannan tashe tashen hankula sun zo bayan isar rukunin farko na dakarun da shugaban Amirka GWB yayi alkawarin turawa a Iraqi. Yayin da ita kuma rudunar sojin Amirka ta fuskanci mummunar asarar a karshen mako inda aka kashe sojin ta sama da 29 tun daga ranar juma´a.