1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An sake naɗa Jacob Zuma a tsohon muƙaminsa a jam’iyyar ANC.

May 15, 2006
https://p.dw.com/p/BuyL

’Yan jam’iyyar ANC ta Afirka Ta Kudu, sun sake naɗa tsohon mataimakin shugaban ƙasar, Jacob Zuma, a muƙamin da yake riƙe da shi a da, na mataimakin shugaban jam’iyyar. Hakan dai ya zo ne mako ɗaya, bayan da wata kotun ƙasar ta wanke shi, daga zargin da ake yi masa na yi wa wata mace fyaɗe. Game da wannan zargin ne dai Zuma ya yi murabus daga muƙaminsa a cikin watan Disamban bara.

Batun dai ya janyo ɓaraka tsakanin mambobin jam’iyyar ta ANC. Har ila yau dai, Jacob Zuman na huuskantar wata shari’ar kuma a kotu, inda ake zarginsa da karɓar cin hanci da rashawa a wani cinikin makamai da aka yi. Amma duk da haka, sake naɗa shi da aka yi, a tsohon muƙaminsa na mataimakin shugaban jam’iyyar ANCin, ya ƙarfafa matsayinsa na yiwuwar gadar shhugaba Thabo Mbeki, wanda wa’adin aikinsa zai cika a shekara ta 2009.