1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An sake wata sabuwar fafatawa tsakanin ƙungiyoyin Falasɗinawa a zirin Gaza.

October 1, 2006
https://p.dw.com/p/Buhj

An sami ɓarkewar wani sabon rikici tsakanin ƙungiyoyin Falasɗinawa masu hamayya da juna a zirin Gaza. Rahotannin da muka samu sun ce dakarun ƙungiyar Hamas sun yunƙuri kwantad da tarzoma da zanga-zanga da ’yan sanda da ma’aikatan gwamnati ke yi don neman a biya su albashinsu. A karawar da ta biyo bayan wannan yunƙurin dakarun Hamas ɗin, mutane 6 ne rahotannin suka ce sun rasa rayukansu, sa’annan wasu 70 kuma suka ji rauni.

A Gaɓar Yamma, ɗaruruwan magoya bayan ƙungiyar Fatah ta shugaban Falasɗinawa Mahmoud Abbas, sun kutsa cikin ginin hedkwatar ƙungiyar Hamas ɗin da ke birnin Ramallah, a wani matakin mai da martani ga abin da ya wakana a Zirin Gaza, inda suka suka cinna wa ginin wuta. Sun kuma yi ta jefad da fyiloli da kujeru daga tagogin ofishin, kafin hayaƙin gobarar da suka tayar ɗin ya tilasa musu barin ginin.