1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An sake yin artabu tsakanin ´yan sanda da masu zanga-zanga a Budapest

September 20, 2006
https://p.dw.com/p/Buiq

Dare na biyu a jere an yi arangama tsakanin ´yan sanda da masu tarzoma a Budapest babban kasar Hungary. Jami´ai sun nunar da cewa mutane kimanin 60 sun samu rauni yayin da aka kame kusan 100. ´Yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye tare da yin feshin ruwa don tarwatsa masu zanga-zangar wadanda ke neman FM Ferenc Gyurcsany ya murabus. An fara zanga-zangar da tarukan gangamin ne bayan da FM ya amsa cewa jam´iyarsa ta yi karya don ta yi nasara a zaben da aka gudanar a cikin watan afrilu. To sai dai FM ya ce zai ba zai yi murabus ba kuma zai ci gaba da aiwatar da tsauraran canje canje akan kasafin kudin kasar. Kasar ta Hungary na samun gibin kasafin kudi na kusan kashi 10 cikin100, abin da ke barazana da shirye shiryenta na shiga jerin kasashe masu amfani da takardun kudi na Euro a shekara ta 2010.