1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An sake zargin sojin Amirka da halaka fararen hula 11 a Iraki

June 2, 2006
https://p.dw.com/p/Buve
Bayan fallasa kisan gillan da ake zargin sojojin Amirka da yiwa fararen hula 24 a garin Haditha, wani faifayen bidiyo ya kunno kai, wanda ke nuni da wani aikin rashin imani da sojin na Amirka suka aikata a Iraqi. Bidiyon ya nuna hoton gawawwakin mutane 11 cikinsu har da kananan yara dukkansu ´yan gida guda. Wadanda suka shaida abin da ya faru sun ce sojojin Amirka suka harbe mutanen a cikin gidansu dake garin Ishaki, bisa zargin cewa wai ´yan ta´adda ne su. A wani labarin FM Iraqi Nuri Al-Maliki yayi kira ga Amirka da ta mika masa dukkan takardun dake hannunta na binciken zargin kisan kiyashin da ake yiwa sojojin Amirkar da aikatawa a garin Haditha a cikin watan nuwamban bara. Maliki ya ce ba abin karbuwa ba ne a kashe fararen hula bisa zargi kawai. Al-Maliki ya ce yanzu kaiwa fararen hula hari ya zama ruwan dare a tsakanin sojojin na Amirka.