1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An saki masu kishin Islama 14 da aka kama a Belgium

December 22, 2007
https://p.dw.com/p/CfGY

Masu shigar ƙara na tarayya a ƙasar Belgium sun ce an saki mutanen nan 14 da aka kama bisa zargin cewa suna shirin ƙwato wani mai goyawa ƙungiyar al-Qa´ida baya daga kurkuku, saboda rashin wata shaida. To sai dai mai magana da yawon ofishin mai shigar da ƙara na tarayya ta ce ana ci-gaba da gudanar da bincike kan makarkashiyar ta kokarin kwato wani ɗan kasar Tunisia mai suna Nizar Trabelsi. A cikin watan satumba na shekara ta 2001 aka kama Trabelsi sannan a shekarar 2004 aka yanke masa hukuncin daurin shekaru 10 a kurkuku bayan an same shi da laifin shirya kai hari kan wani sansanin sojin Amirka dake a ƙasar ta Belgium. Jami´ai sun ce za a ci-gaba da aiki da tsauraran matakan da aka dauka bayan an kame mutanen 14 masu tsattsauran ra´ayin Islama a wani samame da aka kai jiya juma´a.