1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An saki shugaban adawar kasar Uganda a matsayin beli

Ibrahim SaniJanuary 3, 2006

Tuni dai Mr Kizza Besigye ya dukufa wajen yakin neman zaben shugaban kasa jim kadan da sakin na sa

https://p.dw.com/p/BvU4

Bisa rahotanni da suka iso mana daga kasar Uganda, alkalin wata babbar kotu a kasar mai suna Mr John Bosco yace kotu ta dauki matakin bayar da belin Mr Kizza Besigye, bayan data gano cewa ci gaba da tsare madugun adawar kasar ya saba da dokokin kasar ta Uganda.

Bada belin na Mr Besigye yazo ne a ranar farko daya bayyana a gaban kuliya bisa laifin yiwa wata mace fyade, wanda hakan ya fuskanci suka mai tsananin gaske daga magoya bayan shugaban da suka yi tururuwa a kusa da kotun.

Alkalin kotun ya shaidar da cewa tuhume tuhumen da akewa Mr Kizza da suka shafi aiyukan ta´addanci da kuma mallakar makamai ba bisa ka´ida ba, abubuwa da basu kai a tsare shugaban adawar ba, tun da wata babbar kotu a can baya ta bayar da belin sa tare daci gaba da sauraron karar a nan gaba.

Bisa hakan alkalin kotun, John Bosco yace kotun ta bayar da umarnin sakin sa a matsayin beli, sai dai kuma aci gaba da tsare shi bisa wani laifin na daban.

Kafin dai kotun ta zartar da wannan umarni, Mr Kizza Besigye ya kasance a tsare ne a tun daga biyu ga watan disambar bara izuwa jiya litinin da aka bayar da belin nasa.

An dai tsare madugun adawar ne ta Uganda bisa laifuffuka da ake zargin sa da aikata da suka shafi cin amanar kasa da gudanar da aiyuka na ta´addanci a hannu daya kuma da yiwa wata mece fyade.

Rahotanni dai sun shaidar da cewa a ranar juma´ar nan mai zuwa ne ake sa ran ci gaba da sauraron shari´ar da akewa shugaban adawar kasar da suka shafi aiyukan ta´addanci da kuma cin amanar kasa a gaban wata kotun soji.

Bayanai dai sun nunar da cewa jim kadan da sakin Mr Kizza Besigye n, ya shaidawa yan jaridu cewa tsare shi ya sabawa doka kuma laifuffukan da ake zargin sa da aikatawa siyasa ce kawai a cikin su.

Bugu da kari shugaban adawar na jamiyyar FDC ya tabbatar da cewa ba zai yi mamaki ba idan a nan gaba kadan aka sake cafke shi, to amma duk da haka yace babu gudu babu jada baya a game da fafutikar da yake yi na ganin ana tabbatar da adalci da gaskiya a sha´anin shugabanci.

Bayanai dai sun yi nuni da cewa jim kadan da barin sa harabar kotun, Kizza Besigye ya wuce kai tsaye ne izuwa gabashin kasar don ci gaba da gudanar da yakin neman zaben shugaban kasa da aka shirya yi a ranar 23 ga watan fabarairun wannan shekara da muke ciki.

Ya zuwa yanzu dai Mr Kizza Besigye ya kasance a sahun gaba a adawa da shugaba Yoweri Museveni a neman shugabancin kasar a lokacin wannan zabe da aka shiryi a nan gaba kadan.

Bayanai dai sun tabbatar da cewa matukar aka samu Besigye da laifi daya daga cikin guda ukun da ake zargin sa da aikatawa, ka iya kaiwa da soke shi a matsayin dan takarar neman shugabancin kasar, a hannu daya kuma da fuskantar hukunci na kisa.