1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An saki 'yar jaridar Faransa da ake tsare a Somalia

December 25, 2007
https://p.dw.com/p/CgAV

Wasu yan bindiga na ƙasar Somalia sun saki ‘yar jaridar nan ta Faransa da suka sace kwanaki takwas da suka shige a lardin Puntland dake arewacin ƙasar.Wani jami’in gwamnati yace Gwen Le Gouil wanda ke tsara wani shiri na telebijin kan halinda ‘yan gudun hijira suke ciki a Somalia an sake ta ne ba tare da wani sharaɗi ba. Waɗanda suka sace ta tun farko sun bukaci a biya su dala 80,000 kafin su sake ta. A halinda ake ciki kuma ƙasar Burundi ta tura ƙarin dakarunta na wanzar da zaman lafiya kusan 90 zuwa babban birnin ƙasar Somalia Mogadishu,waɗanda zasu haɗe da wasu dakarun nata 100 da ta tura a ranar lahadi. Tura dakarun yana a wani ɓangare ne wani shirin taimakawa dakarun Uganda 1,600 da tun a watan Maris suke ƙasar ta Somalia,ƙarkashin dakarun Ƙungiyar Taraiyar Afrika 8,000 da akayi alkawarin turawa zuwa Somalia.