1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An sako tsohon Firamiyan Haiti daga kurkuku.

July 28, 2006
https://p.dw.com/p/Buou

Rahotanni daga birnin Port Au Prince na ƙasar Haiti sun ce an sako tsohon Firamiyan ƙasar Yvon Neptune daga kurkuku. An dai ɗaure tsohon Firamiyan ne a shekara ta 2004, bayan an same shi da laifin shirya kisan da aka yi wa masu adawa da tsohon shugaban ƙasar Jean Bertrand Aristide. Ofishin manzancin Majalisar Ɗinkin Duniya a Haitin ya yi marhabin da labarin sako tsohon Firamiyan, wanda ya ce yana fama da matsalolin rashin lafiya.

Shi dai Yvon Neotune, ya riƙe muƙamin Firamiyan ƙasar Haitin ne daga shekara ta 2001 zuwa shekara ta 2004. A cikin wannan lokacin, ana zarginsa ne da samun hannu a kisan gillar da aka yi wa mutane kusan 50, masu adawa da gwamnatin shugaba Aristide, a garin Saint-Marc da ke yammacin ƙasar. Hakan kuwa yaa wakana ne makwanni biyu kafin a hamɓarad da shugaban a cikin watan Fabrerun shekara ta 2004.