1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An sako turawa da akayi garkuwa da su a Najeriya

March 27, 2006
https://p.dw.com/p/Bv3x

A Najeriya,yan aware na yankin Naija Delta sun sako maaikatan kanfan9in mai 3 da suke garkuwa da su,Amurkawa 2 da dan kasar Burtaniya daya.

Kakakin gwamnati,Abel oshevere ya fadawa kanfanin dillancin labari na AFP a yau cewa,an mika mutanen 3 ga hannun jamian gwamnati a Warri,inda ya baiyana cewa suna nan cikin koshin lafiya.

Mutanen 3 suna cikin wasu turawa 9 ne da yan aware na Naija Delta suka sace a ranar 9 ga watan fabrairu,sauran 6 tuni an sake su bayan mako daya da sace su.