1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An sako wasu 'yan jaridu da aka yi garkuwa da su

July 18, 2010

Yin garkuwa da mutane ya zama ruwan dare a yankin Naija Delta ta Najeriya

https://p.dw.com/p/OORU
Wani ɗan bindigan Naija DeltaHoto: AP

An sako wasu 'yan jaridar Najeriya guda huɗu da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su a yankin da ake haƙan man fetur na Naija Delta.

Kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya ruwaito sakataren ƙungiyar 'yan jaridun Najeriya Usman Leman wanda ya tabbatar da sakin 'yan jaridun yana cewar babu wani kuɗin fansa da ƙungiyar ko iyalan 'yan jaridar suka biya kafin a sako sun.

A ranar 11 ga wannan watan ne dai, wasu gungun 'yan bindiga suka sace 'yan jaridun tare kuma da neman diyyar Naira miliyan 250 a matsayin kuɗin fansa.

Tuni ƙungiyoyin kare haƙƙin bil Adama na ƙasa da ƙasa suka yi kiran a sako 'yan jaridan. Sace mutane domin neman fansa dai abu ne da ya zama ruwan dare a ƙasar ta Najeriya.

Mawallafi: Babangida Jibril

Edita: Mohammad Nasiru Awal