1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An sako yan Koriya da akayi garkuwa da su a Najeriya

June 8, 2006
https://p.dw.com/p/Buur

Yan ta kife na yankin Naija Delta a taraiyar Najeriya sun saki dukkan yan kasar Koriya ta kudu 5 da sukayi garkuwa da su a jiya laraba.

Cikin wani sako ta yanar gizo ga kafofin yada labarai,kungiyar fafutukar yantar da jamaar yankin Naija Delta ta sanarda cewa,ta saki dukkanin mutanen 5 da karfe 4 na yamma agogon Najeriya.

Kungiyar dai ta neman a sako shugabanta Asari Dokubo da ake tuhumarsa da laifin cin amanar kasa.