1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

AN SAMI KARIN KUDADEN DA AKE KASHEWA KAN HARKOKIN SOJI A DUNIYA.

YAHAYA AHMEDJune 9, 2004

A shekarar bara, an sami habakar kudaden da aka kashe kan sayen makamai da kashi 11 cikin dari, a duk duniya baki daya. Kungiyar nan SIPRI, ta kasar Sweden, mai gudanad da bincike kan zaman lafiya ce ta ba da wadannan alkaluman a cikin rahotonta na shekara-shekara, wanda ta gabatar yau a birnin Stockholm.

https://p.dw.com/p/Bvj0
Shugaba Bush na Amirka, gaban wata masana'antar kera makamai ta kasarsa
Shugaba Bush na Amirka, gaban wata masana'antar kera makamai ta kasarsaHoto: AP

Kafin dai gabatad da wannan rahoton, a birnin Stockholm na kasar Sweden, masharhanta sun yi hasashen cewa, kungiyar SIPRI, za ta dukufad da mafi yawan shafofin sakamakon binciken da ta gudanar ne kan batun yakin Iraqi, saboda babu shakka, a nan ne aka fi kashe makudan kudade kan makamai a shekarar bara. Amma ba haka lamarin ya kasance ba. Ban da dai Iraqin, rahoton na kuma nuna cewa, an sami manyan rikice-rikice 18 a duniya, 8 daga cikinsu a nahiyar Asiya. A daura da rikicin Iraqi da na Kashmiri, duk sauran manyan rikice-rikicen da suka wakana a shekrar baran, na cikin gida ne.

Rahoton dai, ya nanata cewa, tun karshen yakin cacar baka, da kuma 1997, ba a taba samun karancin yawan yake-yake a duniya kamar a shekarar ta bara ba. Amma fa, wannan ba wata alama ce ta samun sassaucin tsamari ba, sabo da rikicin Iraqi kawai, ya habaka kudin da ake kashewa kan makamai fiye da kima. Sakamakon hakan ne dai aka sami karin kashi 11 cikin dari, na kudaden da aka kashe kan makamai a bara din. A duk duniya baki daya, inji rahoton, kudin da aka batar kan makamai ya kai dolar Amirka biliyan dari 9 da 56. Amirka kuma, ita ta kashe fiye da rabin wadannan kudaden. Abin da za a iya la’akari da shi a nan dai shi ne, kudin da kasashe masu arzikin masana’antu suka kashe kan makamai a shekarar bara, ya ninka na wanda suka bai wa asusun taimakon raya kasashe sau 10. Kamar yadda Alyson Bailes, shugaban kungiyar ta SIPRI ta bayyanar, an sami gagarumin bambanci tsakanin alkaluman shekarar bara da na shekara ta 2002:-

"A shekarar bara, mun yi ta tattaunawa ne kan karfin sojin Amirka da kuma ikon da take da shi a huskar siyasa. Ta dai nuna hakan game da yadda ta mamaye Iraqi. A yanzu kuwa, muna mai da hankalinmu ne kan cikas din da take samu, alal misali a gazawar da take yi na shawo kan matsalolin da suka shafi harkokin tsaro a Iraqin, da kuma yunkurin da take yi na daukan matakan radin kai ba tare da samun goyon baya a huskar siyasa da kuma huskar shari’a ba."

Alyson Bailes dai, ta kara da cewa, babu shakka, kwarjinin Amirka ya dusashe a husakar abokanta a duniya baki daya. Wajibi ne kuwa gareta, da ta yi nazarin kurakuran da ta yi ta koyi kuma darasi daga garesu.

Wata masaniya kimiyyar kungiyar ta SIPRI, Renata Dawn, ta yi dogon nazari kan dalilan da ke janyo yake-yake da kuma hanyoyin shawo kansu. Rikice-rikice dai sun fi muni ne a yankunan da aka dade ana ta fama da su, saboda a ko yaushe, wata sabuwar gwagwarmaya na iya barkewa, kuma kafin a ce kwabo, ta habaka ta yi muni. Ana iya ganin misalan hakan dai a Indonesiya, da Burundi, da Aafghanistan da kuma Liberiya, inji masaniya kimiyyar. A nata ganin dai:-

"Idan akwai wani abin da za mu iya koya daga ababan da suka wakana a shekarar bara, to shi ne:- ba za a iya warware rikici da daukan matakan soji kawai ba. Darasin da za mu iya koya daga Iraq, da Afghanistan, da Kosovo, da Saliyo shi ne:- dakarun kasashen yamma masu makamai na zamani, za su iya cin mayakan sunkuru da yaki a sawwake. Amma, matsalar ita ce tabbatad da zaman lafiya mai dorewa, bayan daukin."

A nan ne kuwa, Majalisar Dinkin Duniya za ta iya shigowa cikin lamarin. Amma ita ma a cikin shekarun baya, angizonta ya ragu ainun.

Rahoton kungiyar ta SIPRI dai ya kunshi labarai ne masu ta da hankali, kan kera makamai da kuma sumogansu, makaman da suka hada har da na kare dangi. Shugaban kungiyar Alyson Bailes dai ta nuna damuwarta da yadda ake amfani da manufar yakan ta’addanci wajen hujjanta take hakkin dan Adam a sassa daban-daban na duniya.