1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An samu cigaba wajen yaƙi da cutar zazzaɓin cizon Sauro a Afirka

April 23, 2010

Hukumar kula da lafiya ta duniya WHO ta bayyana cewar ƙasashen Afirka na samun gagarumar ci gaba ta fuskar yaƙi da cutar zazzaɓin cizon sauro ko Malariya

https://p.dw.com/p/N4Ev
Shugabar Hukumar Lafiya ta ƙasa da ƙasa Margaret ChanHoto: AP

Hukumar kula da lafiya ta duniya WHO ta bayyana cewar ƙasashen Afirka na samun gagarumar ci gaba ta fuskar yaƙi da cutar zazzaɓin cizon sauro ko Malaria, wadda ke yin sanadiyyar mutuwar kimanin mutane miliyan ɗaya - a duk shekara, tare da janyo cikas ga bunƙasar tattalin arziƙinta. Darektan shirin yaƙi da Malaria a duniya a ƙarƙashin hukumar lafiyar, Rob Newman, wanda ya sanar da hakan, ya danganta ci gaban da aka samun ne da yawan rarraba gidajen sauro, da magungunan da ake yi, game da sauƙaƙa kudaɗen jinyar masu fama da cutar, inda ya bada misali da ƙasar Zambiya, wadda ta yi nasarar kawar da kusan rabin masu fama da zazzaɓin malaria daga shekara ta 2001 zuwa 2008. Ya ce, kwatankwacin nasarar da Zambiya ta samu ne ake da ita a ƙasashe - kamar Nijeriya da Jamhuriyyar Dimoƙraɗiyyar Kongo. Newman ya ƙara da cewar, hatta shi kansa yana mamakin irin ja da bayan da matsalar cutar ta yi  duk kuwa da tsawon shekarun daya shafe yana wannan aiki.

Mawallafi: Babangida Jibril Edita: Yahouza Sadissou Madobi