1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An samu karuwar yan gudun hijira a duniya

June 19, 2007
https://p.dw.com/p/BuIT

Wani rahoto da MDD ta fitar a yau ya baiyana cewa a karon farko cikin shekaru 5 an samu karuwar yawan yan gudun hijira a duniya.

Rahoton yace yawan jamaa dake tserewa daga yakin Iraki ya janyo karin yawan yan gudun hijirar.

Komishinan kula da yan gudun hijirar yace yanzu haka akwai kimanin yan gudun hijira miliyan tara da dubu dari tara a duniya baki daya wanda hakan kari ne da kashi 14 cikin dari daga 2005.

Ya zuwa karshen shekara 2006 yan Iraqi miliyam daya da rabi ne suka nemi zaman mafaka a wasu kasashe.

Rahoton ya kuma baiyana cewa yawan wadanda suka tagaiyara cikin kasashensu kuma ya karu zuwa miliyan 24 da rabi.

Baya ga kasar Iraki tashe tashen hankula a Lebanon da East Timor da Sudan da Sri Lanka sun haddasa karin yawan yan gudun hijira inji rahoton.