1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An shiga kwanaki uku na ƙarshe a taron muhalli a birnin Bali

December 12, 2007
https://p.dw.com/p/CaUG
An shiga zagaye na karshe a babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya kan muhalli da ke gudana a tsibirin Bali na ƙasar Indonesia, inda babban sakataren MƊD Ban Ki Moon ya yi kira da a amince da wata yarjejeniyar yaƙi da dumamar doron ƙasa kafin shekara ta 2009. Ministocin kare muhalli da wasu shugabanin kasashe zasu amfani da kwanaki uku na ƙarshen babban taro don tsara wani daftarin aiki na yaki da sauyin yanayi bayan shekara ta 2012, lokacin da wa´adin yarjejeniyar birnin Kyoto ya ke ƙarewa. A wani lokaci yau laraba ministan kare muhalli na Jamus Sigmar Gabriel zai yiwa taron jawabi. Da farko Firaministan Australiya Kevin Rudd ya miƙawa sakatare janar na MƊD Ban Ki Moon yarjejeniyar Kyoto da ya sanyawa hannu. Yanzu haka dai Amirka ce kaɗai wata kasa mai arzikin masana´antu da ba ta rattaba hannu kan wannan yarjejeniya don rage fid da gurbataccen hayaki mai dumama yanayi ba.